Monday, 21 December 2015

FALALAR WANDA YA TABBATAR DA TAUHIDI


Dukkan yabo da godiya da kirari sun tabbata ga Allah, taimakonsa da gafararsa muke nema,
kuma muna neman tsarinsa daga shirrin kawukanmu da munanan ayyukanmu. Wanda Allah ya shiryar
babu mai vatar da shi, wanda kuma ya vatar to babu mai shiryar da shi. Kuma ina shaidawa babu abin
bauta da gaskiya sai Allah, shi kaxai ne ba shi da abokin tarayya. Kuma ina shaidawa cewa, Annabi
Muhammad bawansa ne manzonsa ne. (Ya ku waxanda suka yi imani ku ji tsoron yadda ya cancaci
a ji tsoronsa, kada ku mutu face kuna musulmi). (Ya ku mutane ku ji tsoron Ubangijinku wanda
ya halicceku daga rai guda xaya, kuma ya ya halicci matarsa daga gare shi, kuma ya yaxa maza da
mata daga garesu (su biyu). Ku ji tsoron Allah wanda kuke yiwa junanku magiya da shi, (kuma ku
kiyaye) zumunci. Lalle Allah mai kula ne da ku). (Ya ku wanxanda suka yi imani ku ku ji tsoron
Allah kuma ku faxi magana ta daidai. Sai Allah ya gyara muku ayyukanku, kuma ya gafarta muku
zunubbanku. Wanda ya bi Allah da Manzonsa haqiqa ya rabauta rabauta mai girma). Bayan haka,
lalle mafi gaskiyar magana maganar Allah, kuma mafi kyawon shiriya shiriyar Annab Muhammad
صلى الله عليه وسلم) ). Kuma mafi shirrin al'amura (a addini) qagaggunsu, kuma duk wani qagaggen abu (addini) bidi'a
ce, duk wata bidi'a vata ce, duka wani vata kuma yana wuta.
Bayan haka, ya ku bayin Allah! Ina yi muku wasiyya, da ni kaina, da tsoron Allah a voye, da
kuma a fili. Sannan ku sani cewa, zuciyar mumini ba ta gyaruwa, sai da wani abu mai girma, kuma
babu wanda zai kuvuta daga duniya, sai da tabbatar da shi. Allah ya yi bayanin sa a cikin littafinsa,
kuma Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم) ya yi bayanin sa a cikin sunnarsa, bayani mai warkarwa, mai gamsarwa, shi
ne kaxaita Allah mai girma, da bautata masa shi kaxai, babu mai tarayya da shi, da kuma tsantsanta
aiki gare shi.
Tauhidi shi ne tushe mai girma, wanda sama da qasa suka tsaya a kansa. Ubangiji ya ce,
.[ الأنبياء: ۲۲ ] L ¿ ¾ ½ ¼ » º ¹ ¸¶ μ ´ ³ ² ± ° M (Da a ce akwai abubuwan bauta a cikinsu (sama da qasa), ba Allah ba, da sun vaci. Tsarki ya
tabbata ga Allah Ubangijin al-arshi, daga abin da suke siffantawa).
Saboda da shi ne aka halicci bil Adama da iskokai, kuma aka aiko manzanni, tsira da aminci su
tabbata a gare su. Allah ya ce:
FALALAR WANDA YA TABBATAR
DA TAUHIDI
Manufofin
huxubar
• Bayanin muhimmancin tauhidi da falalarsa.
• Bayani kan cewa tauhidi shi ne sinadarin tsirar bawa
ranar tashin qiyama, da kuma yafe masa laifukansa.
• Bayani kan cewa tauhidi sababin juyar da bala’i da
fitina ne.
• Bayani kan muhimmancin sanin tauhidi, da kuma
shirka da nau’ikanta.
Huxuba Ta Farko
hausaminbar.com
www.hausaminbar.com
11
.[ الذاريات: ٥٦ ] L I H G F E D C M (Ban halicci aljannu da bil Adama ba, sai don su bauta mini).
Ma’ana, don su kaxaita ni.
Kuma saboda shi ne, har yau, aka halicci aljanna da wuta. Duk wanda ya tabbatar da shi, sannan
ya mutu, zai shiga aljanna; duk wanda bai tabbatar da shi ba, ba zai shiga aljanna ba.
Daga Uthman, Allah ya yarda da shi, ya ce, Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم) ya ce, “Duk wanda ya mutu,
alhali yana sanin cewa babu abin bautawa bisa cancanta, sai Allah, zai shiga aljanna.” [Muslim ya
rawaito shi].Kuma saboda shi ne jihadi ya tsayu.
Tauhidi yana da falaloli masu yawa. Daga cikinsu: Lallai yana kankare laifuka, kuma yana hana
ma’abocinsa ya dawwama a wuta. An rawaito daga Ubadah, Allah ya yarda da shi, daga Manzon
Allah ( صلى الله عليه وسلم) ya ce, “Duk wanda ya shaida babu abin bauta bisa cancanta, sai Allah, halin kasancewarsa
shi kaxai, babu mai tarayya da shi, kuma lallai Muhammad bawansa ne, Manzonsa ne, kuma Isa
bawan Allah ne, Manzonsa ne, kuma kalmarsa ce da ya jefa wa Maryam, kuma ruhi ne daga gare shi.
Kuma aljanna tabbas ce, kuma wuta tabbas ce, Allah zai shigar da shi aljanna, bisa abin da ya kasance
na aiki.” [Bukhari ya ruwaito shi]
Kuma yana daga cikin falalarsa, da shi ne bawa yake kusantuwa zuwa ga Ubangijisa. Allah
Ta’ala ya ce:
.[ آل عمران: ۱۹ ] L ML K J I H M (Haqiqa addini a wajen Allah, shi ne musulunci).
Kuma da shi ne cikakken aminci yake samuwa, da kuma cikakken shiriya ga bawa, a duniya da
lahira. Ubangiji ya ce,
.[ الأنعام: ۸۲ ] L , + * ) ( ' & % $ # " ! M (Waxanda suka ba da gaskiya, kuma ba su cuxanya ban-gaskiyarsu da zalunci ba, irin waxannan
suna da cikakken aminci, kuma su ne shiryayyu).
Kuma Allah ya ce,
.[ الأنبياء: ۱۰۳ ] L 7 6 5 4 3 2 1 0 / . - , M (Firgici mafi girma, ba ya baqanta musu zuciya, kuma mala’iku suna tarbar su, suna cewa,
“Wannan shi ne yininku, wanda kuka kasance ana alqarwanta muku).
Kuma yana daga cikin falalar tauhidi, shi ne, gwargwadon yadda ka tabbatar da tauhidi, ka
tsantsanta ibada ga Allah, kuma ka nesanci shirka ta fili da ta voye, gwargwadon yadda za ka samu
aminci da shiriya. Don haka, za ka ga mumini, wanda ya kaxaita Allah, ya fi mutane samun aminci a
duniya, kuma ya fi mutane samun aminci a lahira. Kamar yadda kuma, tauhidi sanadi ne na juyar da
bala’i da fitintinu. Ubangiji yana cewa,
.[ الأنبياء: ۹۸ ] L } | { z y x w v u t s r M (Lallai ku, da kuma abin da kuke bautawa, koma-bayan Allah, makamashin jahannama ne….”
har a zuwa faxinsa, “Haqiqa waxanda kalmar yabo ta rigaya gare su, daga gare mu, su waxanda ake
nesantawa ne daga gare ta).
Ga Annabin Allah, Ibrahim, badaxin Allah, Allah ya raba shi da wuta, a lokacin da aka jefa shi
a cikin wuta. Ubangiji ya ce,
» º ¹ ¸ ¶ μ ´ ³ ² ± ° ¯ ® ¬ « ª © ¨ § M
.[۷۱ – الأنبياء: ٦۹ ] L ¿ ¾ ½ ¼
hausaminbar.com
www.hausaminbar.com
12
(Muka ce, “Ya ke wuta! Ki zama sanyi da aminci a kan Ibrahim. Kuma suka nufi kaidi a gare
shi, sai muka tseratar da shi, da Annabi Luxu, zuwa qasa wadda muka sanya albarka a cikinta ga
talikai).
Ya ku bayin Allah! Lallai mafiya shiriya cikin mutane, kuma mafiya samun aminci a cikinsu,
su ne annabawa da manzanni, saboda tabbatar da tauhidi da suka yi, da kuma tsantsanta bautarsu ga
Allah. Ga Annabi Dawud, Allah Ta’ala ya siffanta shi da komawa zuwa gare shi. Ya ce,
.[ ص: ۱۷ ] L - , + *) ( ' & % $ # " ! M (Ka yi haquri a kan abin da suke faxa, kuma ka ambaci bawanmu Annabi Dawud, ma’aboci
qarfi. Lallai shi mai yawan komawa ne zuwa ga Allah).
Ku sani, ya bayin Allah, tauhidi ya kasu zuwa gida uku: Tauhidin kaxaita Allah da aikinsa;
tauhidin kaxaita Allah da aikin bayi, wato ibada; da tauhidin kaxaita Allah cikin sunayensa da
siffofinsa. Haqiqa Allah ya haxa waxannan nau’ika guda uku, a cikin faxinsa,
.[ مريم: ٦٥ ] L . - , + * )( ' & % $ # " ! M (Ubangijin sammai da qasa da abin da yake tsakaninsu, ka bauta masa, ka jure wa ibadarsa.
Shin ka san wani a matsayin takwara gare shi?).
Kuma tabbatar da tauhidi da rabe-rabensa guda uku, ya zo da dama a cikin Alqur’ani mai
girma. Daga ciki, akwai faxinsa,
L 3 2 1 0 / . - , + * ) ( ' & % $ # " ! M
.[٤ – [الإخلاص: ۱
(Ka ce, “Shi Allah, shi kaxai ne. Allah wanda ake buqatuwa zuwa gare shi, bai haifa ba, kuma
ba a haife shi ba, kuma babu wani da ya zama tamka gare shi).
Kuma Allah ya ce,
¿ ¾ ½ ¼» º ¹ ¸ ¶ μ ´ ³ ² ± ° ¯ ® ¬ « M
! Ó Ò Ñ Ð Ï ÎÍ Ì Ë Ê É È Ç Æ Å ÄÃ Â Á À
.[۳٤ – إبراهيم: ۳۲ ] L 2 1 0 / . -, + * ) ( ' &% $ # "
(Allah wanda ya halicci sama da qasa, kuma ya saukar da ruwa daga sama, sannan ya fitar da
‘ya’yan itatuwa da shi, don arziki gare ku, kuma ya hore jiragen ruwa, don su gudana a cikin teku, da
izininsa, ya kuma hore muku qoramu. Kuma ya hore muku rana da wata masu gudu ba qaqqautawa,
kuma ya hore muku dare da yini. Kuma ya ba ku daga duk abin da kuka roqe shi. Kuma idan za ku
lissafa na’imar Allah to ba za ku iya qididdige ta ba. Lallai xan Adam mai yawan zaluntar kansa ne,
mai yawan butulci).
Kuma Allah ya ce,
.[ الشورى: ۱۱ ] L 8 7 6 5 43 2 1 M (Babu wani abu da yake kamarsa, kuma shi mai ji ne, mai gani ne).
An karvo daga Abu Huraira, ya ce, Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم) ya ce, “Ubangiji ya ce, “Ka ciyar, zan
ciyar da kai.” Kuma ya ce, "Hannun Allah a cike yake, ciyarwa ba ta tauye shi, mai yaye dare da rana.
Ya ce, “Ku ba ni labari kan abin da Allah ya ciyar, tunda ya halicci sama da qasa. Lallai haka bai
tauye abin da yake hannunsa ba. Kuma al-arshinsa ya kasance a kan ruwa, sikeli yana hannunsa, yana
saukar da shi, yana xaga shi.” [Bukhari ya ruwaito shi].
Allah ya yi albarka gare ni, tare da ku, cikin Alqur’ani mai girma, kuma Allah ya amfanar da
ni, da ku, da abin da yake cikinsa, na ayoyi da tunatarwa mai azanci. Shi majivincin haka ne, kuma
mai iko a kan haka. hausaminbar.com
www.hausaminbar.com
13
Huxuba Ta Biyu
Godiya ta tabbata ga Allah, Ubangijin talikai, kuma tsira da aminci su tabbata ga mafi xaukakar
Annabawa da Manzanni, Annabinmu, Muhammad, da iyalensa da sahabbansa gabaxaya.
Bayan haka, ya ‘yan uwa! Lallai tauhidi yana da abubuwan da suke warware shi masu yawa,
wajibi ne a kan mutum ya yi taka-tsantsan da su, saboda aukawa cikinsu, yana warware tauhidi,
kuma sanadi ne na shigar mutum wuta. Daga ciki, akwai shirka da rabe-rabenta. Babbar shirka tana
warware tauhidi gabaxaya. Qaramar shirka kuma tana warware cikar tauhidi.
Haka nan, roqon wanin Allah buqatar da Allah kaxai yake da ikon yin ta, kamar mutum ya
nemi aljani ko waliyyi ko shehi, ya yaye masa cuta, ko ya jawo masa amfani, wannan shirka ce
mai girma, wadda take warware tauhidi baki xaya. Haqiqa Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم) ya nuna cewa, adu’a
ibada ce, kamar yadda ya ce, “Adu’a ita ce ibada.” [Tirmizi da Ahmad suka rawaito] Hakanan, yana
daga shirka babba, abin da mutane suke yi a yau, na xawafi da duqufa a kan qaburan bayin Allah na
qwarai, da kuma neman biyan buqata daga gare su, koma-bayan Allah. Allah Ta’ala ya ce,
[ الأحقاف: ٥ ] L Ï Î Í Ì Ë Ê É È Ç Æ Å Ä Ã Â Á À ¿ ¾ ½ M (Wanene ya fi vata, sama da wanda yake roqon wani koma-bayan Allah, wanda ba zai amsa
masa ba, har tashin qiyama, su sun shagala ga barin addu’arsu su?).
Daga ciki, akwai zuwa wajen bokaye, da ‘yan tsibbu, da ‘yan duba, da kuma gaskata su cikin
abin da suke faxi na da’awar sanin gaibu. Ubangiji Ta’ala ya ce,
.[ الأنعام: ۱۷ ] L Ó Ò Ñ Ð Ï Î Í Ì Ë ÊÉ È Ç Æ Å Ä Ã Â Á M (Idan Allah ya shafe ka da cuta, babu mai yaye ta, sai shi, idan kuma ya shafe ka da alheri, to
shi mai iko ne a kan komai).
Daga ciki, akwai shirka ta nufin wanin Allah, kamar mutum ya nufi duniya, ko son a sani, ko a
gani, da aikinsa. Allah Ta’ala ya ce,
\ [ Z Y X W V U T S R Q P O N M L K J I H G M
.[۱٦ – هود: ۱٥ ] L g f e d c b a ` ^]
)Duk wanda yake nufin rayuwar duniya da adonta, za mu cika musu ayyukansu a cikinta, su
ba za a tauye su a cikinta ba. Irin waxannan ba su da komai a lahira, sai wuta, abin da suka aikata a
cikinta ya rushe, kuma abin da suka kasance suna aikatawa lalatacce ne).
Daga ciki, akwai shirka ta biyayya. Ita ce biyayya ga abin halitta wajen halatta abin da Allah
ya haramta. Allah Ta’ala ya ce,
.[ التوبة: ۳۱ ] L ¯ ® ¬ « ª © ¨ M (Sun riqi malamansu, da masu bautarsu, iyayen giji, koma-bayan Allah).
Kamar yadda Annabi ( صلى الله عليه وسلم) ya fassara wa Adiy xan Hatim, lokacin da ya tambaye shi. Ya ce,
“Ba ma bauta musu!” Sai Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم) ya nuna masa cewa, bautar ita ce, yi musu biyayya a
kan savon Allah, da janja hukuncin Allah. Ya ce, “Ba suna haramta abin da Allah ya halatta ba, sai
kuma ku xauke su a matsayin haram, kuma suna halatta abin da Allah ya haramta, sai ku xauke shi a
matsayin halal?” Sai ya ce, “Na’am!” Sai ya ce, “Wannan ita ce bauta musu.” [Tirmizi da Xabarani
suka rawaito shi].
Daga cikin akwai shirka ta soyayya wadda take tilasta girmamawa da rusunawa da qasqantar
da kai, wanda ba su cancanta a yi su ba, sai ga Allah shi kaxai. Duk sanda bawa ya yi irin wannan
hausaminbar.com
www.hausaminbar.com
14
soyayya ga wanin Ubangiji, to haqiqa ya yi shirka mai girma. Ubangiji yana cewa,
.[ البقرة: ۱٦٥ ] L ^] \ [ Z Y XW V U T S R Q P O N M M (Daga cikin mutane, akwai waxanda suke riqar kishiyoyi koma-bayan Allah, suna son su,
kamar yadda suke son Allah. Su kuwa waxanda suka yi imani, sun fi tsananin soyayya ga Allah).
Ya ku bayin Allah! Ku sani cewa, Allah Tabaraka Wa Ta’ala, ba ya gafarta a yi shirka da shi.
Ubangiji ya ce,
.[ النساء: ٤۸ ] L ے~ } | { z y x w v u t s r M (Lallai Allah ba ya gafarta a haxa wanin Allah da shi, amma yana gafarta abin da yake komabayan
haka, ga wanda ya so).
Kuma ya ce,
7 6 5 4 3 2 1 0 / . - , + * ) ( ' &% $ # " ! M
.[ الحج: ۳۱ ] L )Duk wanda ya haxa wani da Ubangiji, to kamar wanda ya faxo daga sama ne, sai tsuntsaye
suka wabce she, ko iska ta yi wurgi da shi a wani waje mai nisa).
Kuma Ubangiji ya ce,
.[ المائدة: ۷۲ ] L Z Y X W V UT S R Q P O N M L K J M (Duk wanda ya haxa Allah da wani, haqiqa Allah ya haramta masa shiga aljanna, kuma
makomarsa ita ce wuta, kuma azzalumai ba su da mataimaka).
Idan Allah ba ya yarda da shirka, sai dai tauhidi, kuma ba ya gafarta shirka, to lallai azabar
masu yin shirka, mai girma ce. Azabarsu ita ce wuta, azabarsu ita ce wulaqanci a duniya da lahira.
Waye a cikinmu - ya bayin Allah - ba ya son kuvuta a duniya da lahira? Waye a cikinmu, ba ya son
ya shiga aljanna ba tare da hisabi ko azaba ba? Waye a cikinmu, ba ya son ya rayu, rayuwa mai daxi
a duniya, kuma ya kuvuta ranar da dukiya da ‘ya’ya ba sa amfani?
Saboda haka, ku lazimta wa kanku tabbatar da tauhidi ga Allah, da tsantsanta bauta gare shi.
Kuma ku koyi hakan, kuma ku kula da abin da malaman musulunci da jagororin sunna da jagororin
wannan kira suka rubuta a kan waxannan manya-manyan mas’aloli na tauhidi. Domin, duba littattafan
tauhidi, haske ne a cikin zukata, kuma shiriya ce ga rayuwa, kuma a cikin tauhidi nagarta take ga
xaixaikun mutane da al’umma. Kada duniya ta shagaltar da kai ga barin wannan tushe mai girma,
wanda ya tattare komai da komai, wanda saboda shi aka aiko Annabawa da Manzanni, kuma saboda
shi aka halicci aljanna da wuta. Ku bai wa tauhidi haqqinsa, kuma ku gabato wajen koyon sa, tun
daga wannan lokacin, tare da niyya ta gaskiya. Ku koyi tauhidi a dunqule, da kuma a rarrabe, don
kada ku auka cikin abinn da mafi yawan mutane suka auka ciki na jahilci ko barin tauhidi.
Ina roqon Ubangiji, ya inganta mana niyyoyinmu, ya kuma inganta mana addininmu, ya kuma
inganta mana duniyarmu. Lallai shi mai kyauta ne, mai karamci. hausaminbar.com
www.hausaminbar.com

Friday, 18 December 2015

MUHIMANCIN ADDU'A DA SHARADDANTA

Dukkan yabo ya tabbata ga Allah muna yabon Sa muna neman taimakonsa, muna neman
gafararsa, muna neman tsarinsa. Duk wanda Allah Ya shiryar babu mai vatar da shi wanda kuma ya
vatar babu mai shiryar da shi kuma ina shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah shi kaxai ba
shi da abokin tarayya. Kuma ina shaidawa cewa, Annabi Muhammadu bawansa ne manzonsa ne (ya
ku waxanda suka yi imani kuji tsoron Allah yadda ya cancanci a ji tsioronsa, kada ku mutu face kuma
musulmi) (ya ku mutane kuji tsoron Ubangijimku wanda ya halicceku daga rai guda xaya, kuma ya
halicci matar sa daga gare shi, kuma ya yaxa maza da mata daresu (su biyu) ku ji tsoron allah wanda
kuke yi wa junanku magiya dashi (kuma ku kiyaye) zumunci lalle Allah mai kulane daku) (yak ku
waxanda kuka yi imani ku ji tsoron Allah kuma ku faxi Magana ta daidai, sai Allah ya gyara muku
ayyukanku kuma ya gafarta muku zunubanku, wanda yabi Allaha da Manzon Allah haqiqa ya rabauta
rabauta mai girma). Bayan haka, lalle mafi gaskiyar magana maganar Allah, kuma mafi kyawun
shiriya shiriyar Annami Muhammad ( صلى الله عليه وسلم) kumamafi sharin al’amura (a addini) qagaggunsu. Kuma
duk wani qagaggen abu (a addini) bidi’a ce, kuma duk warta bidi’a vata ce, kuma duk wani bata yana
wuta.
Bayan haka;
Ya ku bayin Allah, ku sani cewa dukkan halitta mabuqata ne zuwa Ubangijinsu wajen janyo
musu amfani da ije musu cututtuk, domin gyara addininsu da duniyarsu. Kuma kuma kamalar mutum
tana tattare da tabbatar da bautarsa ga Allah mai girma da xaukaka, kuma duk sanda bawa ya qara
tabbatar da bautarsa sai kamalarsa ta qaru, kuma darajarsa ta xaukaka, kuma Allah mai girma da
xaukaka yana jarrabar bayinsa da wasu abubuwa masu bijirowa da sukan tura su zuwa qofarsa su
neman agajjinsa, kuma buqatuwa zuwa ga Allah, ita ce haqiqanin wadatuwarsa. Kuma qaunar bauta
da babbar manufarta, da kuma qasqantar da kai ga Allah mai tsarkin mulki shi ne xaukakar da ba
za a iya gasa da ita ba. Kuma addu’a ita ce alamar bauta, Allah yana son bayinsa su roqe shi a cikin
dukkannin buqatunsu. Domin ya zo cikin Sahih Musulim daga hadisin Abi Zarr, Allah Ya qara yarda
a gare shi, Allah Maxaukakin Sarki Ya ce: “Ya ku bayina dukkaninku vatattu ne sai fa wanda na
ADDU’A: MUHIMMANCINTA DA
SHARAXANTA
Manufofin
huxubar
• Bayanin ma’anar addu’a da buqatuwar halitta zuwa
gare ta.
• Bayanin hukunce-hukuncenta da sharadanta da
ladubbanta.
• Gargaxi a kan wasu kurakurai dangane da addu’a.
Huxuba Ta Farko
hausaminbar.com
www.hausaminbar.com
16
shiryar da shi, to ku nemi shiriyata, zan shiryar da ku. Ya ku bayina dukkanin ku mayunwata ne, sai
fa wanda na ciyar da shi, to ku nemi ciyarwata, zan ciyar da ku. Ya ku bayina dukkaninku matsiraita
ne, sai fa wanda na tufatar da shi, to ku nemi tufatarwa zan tufatar da ku. Ya ku bayina haqiqa kuna
yin kuskure da dare da rana, ni kuma in gafarta zunubi baki xaya, ku nemi gafara ta zan gafarta
muku...”.
Ya ku bayin Allah, ku yi sani cewa, Allah (S.W.T) ya hore hanyoyin samun rabo, kuma ya
huwace hanyoyin tavewa. Kuma ya jera abubuwa masu faruwa a bisa dalilan faruwarsu, kuma ya
halicci sakamakon da za su haifar. Kuma babu wani abu da yake hukunta kansa da nufinsa. Da ya so
da ya samar da abu ba tare da sababi ba. Allah Ta’ala Ya ce,
[ البروج: ۱٦ ] L ª © ¨ § M
(Shi mai aikatawa ne ga abin da ya yi nufi).
Kuma Maxaukakin Sarki ya ce:
.[ الأعراف: ٥٤ ] L w v u t s rq p o n M Ma’ana: (Lalle halitta da umarni na shi ne. Albarkatun Allah sun yawaita. Ubangijin talikai).
Don haka, addu’a dalili ne babba na rabauta da alherai da albarkatai. Kuma dalili ne na na yaye
baqin ciki, da sharri da bala’i. Tirmizi ya ruwaito daga Ibn Umar (R.A) ya ce, “Addu’a tana amfani
ga abin da ya sauka, da ma wanda bai sauka ba.”
Addu’a tana daga cikin qaddara, kuma sabab ce daga sabubba masu amfani, masu janyo alheri
su ije dukkan sharri.
Haqiqa Allah ya yi umarni da addu’a a cinkin ayoyi masu yawa, ya ce,
.[ غافر: ٦۰ ] L ; : 9 8 7 6 5 4 3 21 0 / . - M (Kuma Ubangijinka ya ce, ku roqe ni, na amsa muku. Haqiqa waxanda suke girman kai ga
barin bautata za su shiga wutar Jahannama suna qasqantattu).
Ya ku bayim Allah! Ku sani cewa haqiqa yin addu’a shi ne: tsananta kwaxayi ga Allah Ta’ala
wajen neman biyan buqatun duniya da na lahira da yaye baqin ciki da kaxe sharri, da bala’i na duniya
da lahira. Da addu’a ne bautar Ubangijin talikai takan tabbata, domin ta qunshi ratayuwar zuciya da
Allah Ta’ala da Ikhlasi gare shi, da rashin waiwayen wani ba shi ba.
Addu’a ta qunshi sakankancewa da cewa Allah mai cikakken iko ne, babu wani abu da zai
gajiyar da shi, babu wani abu da zai vuya a gare shi, mai rahama mai jinqai. Rayayye ne, mai isa da
zatinsa, ma’abocin alheri har abada, ba a iyakance baiwarsa da alherinsa. Taskokin albarkatunsa ba
sa qarewa.
Addu’a ta qunshi buqaturuwar bawa da tsananin matsiwarsa zuwa Ubangijinsa, waxannan
abubuwa ne haqiqanin ma’anar ibada.
Ya ku bayin Allah! Haqiqa ximbin nassoshi na hadisazan Annabi sun zo game da falalar
addu’a. Daga cikinsu akwai abin da Abu Dawud da Tirmizi suka ruwaito daga Nu’uman bn Bashir,
Allah ya qara yarda a gare su daga Annabi ( صلى الله عليه وسلم) ya ce: “Addu’a ita ce ibada.” Tirmizi ya ce: hadisi ne
kyakkyawa ingantacce.
Kuma an karvo daga Abu Hurairah Allah ya qara yarda a gare shi ya ce daga Annabi ( صلى الله عليه وسلم) ya
ce: “Babu wani abu da ya fi girma wajen Allah kamar addu’a.” Ahmad da Tirmizi da Ibn Majah da
Ibn Hibbana suka rawaito.
Hakanan ana rawaito daga Abu Hurairah (R.A) ya ce, Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم) ya ce: "Haqiqa Allah
mai girma da buwaya yana cewa: “Ni ina wajan zaton bawana gare ni, kuma ni ina tare da shi (da sani hausaminbar.com
www.hausaminbar.com
17
na) idan ya ambace ni”. Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi kuma lafazinsa ne. Haka nan Tirmizi
da Nisa’i da Ibn Majah duk sun rawaito shi.
An karvo daga Ubadah xan Samit (R.A) cewa, Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم) ya ce, “Babu wani musulmi
a ban qasa da zai roqi Allah da wata addu’a face ya ba shi ita, ko ya kaxe masa wani mummunan abu
a madadinta, matuqar ba ya roqi wani abin laifi ba ko yanke zumunci". Sai wani mutum daga cikin
mutanen ya ce: "Ashe za mu yawaita ke nan". Sai ya ce: “Allah Shi ne mafi yawaita wa.” Tirmizi ya
rawaito kuma ya inganta shi.
Ya ku bayi Allah! Ku sani cewa ba a roqon kowa sai Allah, ba wani mala’ika makusanci ga
Allah, ko wani Annabi mursali, ko wani waliyyi nagartacce. Kuma duk wanda ya kirayi wani abin
halitta ba Allah ba, Annabi ne ko mala’ika, ko waliyyi, ko aljan, ko kabari, ko makamancinsa, to
haqiqa ya yi shirka da Allah Ta’ala, cikin ibadarsa, shirka da za ta fitar da shi daga musulunci. Allah
Ta’ala Ya ce:
.[ الجن: ۱۸ ] L O N M L K J I H G M (Kuma haqiqa masallatai na Allah ne, don haka kada ku kira wani tare da Allah).
Kuma maxaukakin sarki ya ce,
.[ المؤمنون: ۱۱۷ ] L Ê É È Ç Æ ÅÄ Ã Â Á À ¿ ¾ ½ ¼ » º ¹ ¸ ¶ M (Kuma wanda ya kira yi wanin Ubangijin tare da Allah wanda ba shi da wani dalili (ga bauta
masa), lallai to wannan hisabinsa yana wajan ubangijinsa, lallai kafirai ba su rabauta ba).
Kuma Ya ce,
.[ يونس: ۱۰٦ ] L ß Þ Ý Ü Û Ú Ù Ø× Ö Õ Ô Ó Ò Ñ Ð Ï Î M “Kada ka kirawo wani ba Allah ba, wanda ba zai amfaneka ba, kuma ba zai cutar da kai ba, idan
kuwa ka aikata haka, to lallai kai kana cikin azzalumai). Kuma ya ce,
: 9 87 6 5 4 3 2 10 / . - , + *) ( ' & % $ # " ! M
.[ يونس: ۱۰۷ ] L < ;
(Kuma idan Allah ya jarrabe ka da cuta to babu mai yaye maka ita face shi, idan kuma ya nufe
ka da alheri to babu mai mai da falalarsa, yana samar wanda ya so daga bayinsa da shi, kuma shi ne
mai gafara mai Jinqai).
Kuma Allah Ta’ala Ya ce,
.[ سبأ: ٤۰ ] L + * ) ( ' & % $ # " ! M “Kuma ranar da zai tashe su gaba xaya sannan ya ce da mala’ikunsa, shin waxannan ku ne suka
kasance suna bautawa? Sai su ce tsarki ya tabbata a gare ka, kai ne majivincinmu, ba su ba. Kaxai sun
kasance suna bautawa aljannu ne mafi yawancinsu masu ba da gaskiya ne da su.”
Ya ku Musulmi! Haqiqa addu’a tana da lokuta na musamman, kuma aka fi qaunar amsa ta a
cikinsu waxanda su ne; addu’a a cikin sujjada. Daga Abu Huraira Allah ya yarda da shi, daga Annabi
صلى الله عليه وسلم) ) ya ce, “Lokacin da bawa ya fi kusa da Ubangijinsa, shi ne lokacin da yake sujjada. Don haka, ku
yawaita addu’a a cikinta.” Muslim ne ya rawaito shi.
Kuma an karvo daga Ibn Abbas (R.A.), ya ce: MAnzon Allah ( صلى الله عليه وسلم) ya ce: “Lalle haqiqa ni
an hana ni in karanta Alqur’ani a cikin ruku’u ko sujjada. Amma ruku’u to ku girmama Ubanjigi a
cikinsa. Ita kuma sujjada, to ku yi matuqar qoqari wajen addu’a a cikinta, lallai ya dace amsa muku.”
Muslim ne ya rawaito shi.
Daga ciki: akwai tsakanin kiran sallah da iqama. Domin an rawaito daga Anas (R.A) ya ce:
hausaminbar.com
www.hausaminbar.com
18
Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم) ya ce: “Ba a mayar da addu’a a tsakanin kiran sallah da iqama.” Tirmizi ne ya
fitar da shi, kuma ya ce, hadisi ne kyakkyawa ingantacce.
Kuma gada ciki: akwai yayin da sulusin dare na qarshe ya rage. Domin ya zo a cikin sahihin
Bukhari, Manzon Allah, tsira da aminci su tabbata a gare shi ya ce: “Ubangijinmu kan sauka (irin
saukar da ta dace da shi), kowane dare zuwa saman duniya yayin da sulusin dare na qarshe ya rage,
sai ya ce “Wane ne zai kira ni na amsa masa? Wane ne zai nemi gafara ta na gafarta masa?”.
Daga ciki: akwai qarshen sa'a bayan sallar La’asar ranar juma’a. An rawaito daga Abi Huraira
(R.A) cewa Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم) ya ambaci ranar Juma’a sai ya ce “A cikinta akwai wata sa'a babu
wani bawa Musulmi da zai dace da ita a tsaye yana sallah, yana roqon Allah wani abu face ya ba shi.
Ya yi nuni da hannunsa yana qarantata.” Bukhtari da Muslim ne suka rawaito shi.
Ma’abota ilimi suna da mazhabobi da dama wajen tantance wannan sa'ar ta ranar Juma’a. Amma
mafi inganci shi ne cewa, qarshen sa'a bayan La’asar, kamar yadda yake a cikin hadisin Abi Dawud
da waninsa, Annabi ( صلى الله عليه وسلم) ya ce, (Ranar Juma’a sa'a sha biyu ce, ba za a samun wani Musulmi yana
roqon Allah wani abu a cikinta face ya ba shi. Ku neme ta a sa'a ta qarshe bayan sallar La’asar).
Yana daga guraren amsa addu’a da shari’a ta zo da su: Daren Lailatul Qadari, da ranar Arafa,
da gurin Hajarul Aswad, da yayin saukar ruwan sama, da bayan sallolin farilla, da lokacin shan ruwa
a yayin azumi.
Ya ku bayin Allah! Ku ganimanci falalar Ubangijinku, ku fake zuwa gare shi cikin lamuranku.
Ku xaukaka tafukanku da qasqan da kai, ko a amsa addu’o’inku! Kuma ku rabauta da yardar
Ubangijinku.
Ina faxar abin da kuke ji kuma ina neman gafarar Allah Maxaukakin Mai girma ga kaina da ku,
da a kuma sauran Musulmi daga kowane zunubi. Lallai shi ne Mai yawan gafara Mai yawan jinqai.
Huxuba Ta Biyu
Godiya ta tabbata ga Allah wannan da ya shiryar da majivintansa ga addinin musulunci, ina
yabansa ina gode masa a bisa datarwarsa da shiyarwarsa, ina shaidawa cewa babu abin bautawa da
gaskiya sai Allah shi kaxai, ba shi da abokin tarayya ma’abocin buwaya da girma. Kuma ina shaidawa
cewa Annabu Muhammad Manzon Allah ne amintacce. Allah ka yi salati da sallama a bisa bawanka
da kuma manzonka Muhammadu da alayansa, da sahabansa gabaxaya.
Ku sani ya ku bayin Allah cewa, addu’a tana da sharuxxa waxanda dole sai an cika su kafin
addu’ar bawa ta samu karvuwa wajen Ubangijin sa, su ne kamar haka;
Na farko: Tsarkake tauhidi ga Allah Ta’ala. Allah Ya ce:
.[ غافر: ۱٤ ] L « ª © ¨ § ¦ ¥ ¤ £ M
(Don haka ku kira Allah kuna masu tsarkake addini a gare shi, ko da kafirai sun qi). Kuma
haqiqa ya zo a cikin hadisil Qudusi: “Ya kai xan’adam haqiqa kai da za ka zo mini da cikin qasa na
zunubai, sannan ka gamu da ni ba ka tara bauta ta da wani abu ba, da na zo maka da kwatankwacinta
na gafara.” Tirmizi ne ya rawaito shi.
Na biyu: Nisantar haram a cimarka, da abin sha da tufafi; domin Muslim ya rawaito a cikin
sahihinsa, daga hadisin Abu Huraira (R.A) cewa, Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم) ya ce “Ya ku mutane haqiqa
Allah Ta’ala tsarkakakke ne, ba ya karva sai tsarkakkake. Kuma Allah ya umarci Muminai da abin da
ya umarci Manzanni da shi, sai ya ce, hausaminbar.com
www.hausaminbar.com
19
.[ المؤمنون: ٥۱ ] L } | { z y xw v u t s r q M (Ya ku manzanni ku ci daga daxaxa, kuma ku aikata aiki na gari, haqiqa Ni masani ne da abin
da kuke aikatawa). kuma ya ce,
.[ البقرة: ۱۷۲ ]L [ Z Y X W V U T S R Q P O N M M (Ya ku waxanda suka yi imani, ku ci daga daxaxan abin da muka azurta ku, kuma ku yi godiya
ga Allah in kun kasance shi kaxai kuke bautawa).
Sannan ya ambaci mutum da yake tsawaita tafiya, mai hargitsattsan gashi, mai buxu-buxu, yana
xaga hannayensa zuwa sama, (yana addu’a yana mai cewa): Ya Ubangiji! Ya Ubangiji!! (Alhali)
abincinsa haramun ne, abin shansa haramun ne, kuma tufafinsa haramun ne, kuma an ciyar da shi da
haramu, to ta yaya za a amsa masa.”
Na uku: halartowar zucitya da qarfin fata, domin an rawaito daga Abu Huraira (R.A) daga
Annabi ( صلى الله عليه وسلم) ya ce: “Ku roqi Allah, kuna masu sakankancewa da amsawa, kuma ku sani cewa Allah
baya qarvar addu’a daga zuciya gafalalliya mai wasa”. Tirmizi ne ya rawaito shi.
Na Huxu: ya gabatar da yabo ga Allah da salati ga Annabi ( صلى الله عليه وسلم) gabannin gabatar da buqatarsa,
sabda abin da ya zo a cikin ingatatcciyar sunna game da haka.
Kamar yadda addu’a ta ke da wasu ladabbai da ya kamata bawa ya lura da su yayin da yake yin
addu’a.
Daga waxannan ladubba akwai:
Ya kasance cikin tsarki, domin addu’a zikiri ce, gashi kuma hadisi ya inganta daga Annabi
صلى الله عليه وسلم) ) cewa, ya yi taimama daga garun wani bango domin amsa sallama, sannan ya ce “Na qyamaci na
ambaci Allah ba tare da ina cikin tsarki ba” Abu Dawud ne ya fitar da shi.
Xaga hannaye, saboda abin da ya zo a cikin hadisi “Haqiqa Ubangijinku mai kunya ne, mai
karamci ne, yana jin kunyar bayinsa idan suka xaga hannayensu zuwa gare shi, su mai da su fayau.”
Hakim ne ya fitar da shi, kuma ya inganta shi. Kuma Azzahabi ya goyi bayansa.
Ya qarfafa aniyarsa a kan addu’ar, saboda faxin Annabi ( صلى الله عليه وسلم): “Idan xayanku zai yi addu’a to ya
qarfafa aniyarsa, kada ya ce "Ya Ubangiji to idan ka so ka ba ni", domin ba mai tilasta masa” Bukhari
ne ya fitar da shi.
Ya kirdadi sigogin addu’a da aka rawaito musamman waxanda suka zo cewa sun qunshi Ismul
A’azam, domin ya zo a cikin sahihin Ibn Hibbana daga hadisin Abdullahi bn Buraidah daga babansa
(R.A.) cewa, Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم) ya ji wani mutum yana cewa “Ya Ubangiji ni ina roqonka da cewa
ni ina shaidawa kai kaxai ne Allah, babu abin bautawa da gaskiya sai kai. Kai kaxai ne abin nufi da
buqata, wanda bai haifa ba, ba a haife shi ba, kuma babu wani da ya kasance tamka a gare shi”, Sai
ya ce, “Haqiqa in an tambaye Shi da shi yana bayarwa, kuma idan an roke shi da shi, sai ya amsa”. A
wani lafazin “Haqiqa ka tambayi Allah da sunansa mafi girma.” Hadisi ne ingantacce. A cikin sunana
daga hadisin Anas xan Malik (R.A) cewa, shi ya kasance tare da Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم) yana zaune,
wani sai ya ce, “Ya Ubangiji, ni ina roqon ka da cewa yabo ya tabbata a gare ka, babu abin bautawa
da gaskiya sai kai, Mai baiwa, maqagin sammai da qassai, ya ma’abocin buwaya da girmamawa ya
rayayye, ya tsayayye (da lamuran halitta).” Sai Annabi ( صلى الله عليه وسلم) ya ce, “Haqiqa ya kira Allah da sunansa
mai girma, wanda idan an roke shi da shi yake amsawa, kuma idan an tambaye shi da shi yake
bayarwa”. (hadisi ne ingantace).
Kuma Bukhari da Muslim sun ruwai daga Ibn Abbas, cewa Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم) ya kasance yana
faxa yayin baqin ciki “Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, Ubangijin Al’arshi mai girma, babu
abin bautawa da gaskiya sai Allah Ubangijin sammai da qassai, Ubangijin al’arshi mai karamci"., hausaminbar.com
www.hausaminbar.com
20
Ya ku bayin Allah! Ya wajaba mu dauwama kan addu’o’i. Ba wai loakcin da musubu da bala'i
suka afko ba kaxai, sai dai kamar yadda ya zo a cikin hadisin Annabi wanda Abu Hurairah (R.A) ya
rawaito daga gare shi mai tsira da amincin Allah, ya ce, “Wanda ya ke son Allah ya karva addu'arsa a
lokacin tsanani, to ya yawaita addu’a yayin da yake cikin yalwa.” Tirmizi ne ya rawaito, kuma Hakim
ya inganta shi.
Allah yana cewa,
L ¼ » º ¹ ¸¶ μ ´ ³² ± ° ¯ ® ¬ « ª © ¨ M
.[ [النمل: ٦۲
“Shin wanene wanda yake amsawa mabuqaci yayin da ya kira shi, kuma yake yaye cuta,
kuma yake sanya halifofi a qasa. Shin akwai wani abin bauta tare da Allah. Kaxanne kwarai kuke
wa’azantuwa). .
Kuma Allah Ta’ala Ya ce,
Î Í Ì Ë Ê É È ÇÆ Å Ä Ã Â ÁÀ ¿ ¾ ½ ¼ » M
.[ البقرة: ۱۸٦ ] L (Kuma yayin da bayina suka yambayeka game da ni, to ni makusanci ne, ina amsa addu’ar mai
addu’a idan ya kirani).
Ina addu’o’in da muke yi kafin salloli, da cikin salloli, da bayan salloli? Ina addu’o’inmu a
tarurruka, Ina addu’o’in da muke yi a ciki sirri da kevancewa da tsakiyar dare da gabanin alfijiri da
cikin awoyin qarshen na dare, da ranakun masifa, ko lokacin bala’i? A koyaushe, to ina gafallalu?
Mu kuwa – in banda waxanda Allah ya jiqansu – muna cikinsu. Ina masu addu’a masu qasqantar da
kai, mu ga yaya sakankacewarsu da wannan addu’a, ranar da imani yake kafe a cikin zuqata, ranar
da nagarta da istiqama suke bayyane cikin voyayyun halaye da bayyanannunsu. Xayansu ya kasance
yana addu’a yana mai yankewa da sakankancewa da amsawar Allah ga wannan addu’a. Har wasu
suka shahara tsakanin sahabbai - Allah ya yarda da su - a kan cewa su, ababen amsa addu’ar su ne,
kamar yadda ya ke a qissar Sa’ad xan Abu Waqqas.
Ga dai Sa’id ibn Zaid, xaya daga goma waxanda aka yi musu bushara da aljanna. Wata mata
ta yi da’awa da qage cewa ya qwace mata wani yanki na qasarta, yayin da aka yi masa magana kan
haka, sai ya ce “Yaya haka, alhali ni na ji cewa, wanda ya qwaci taku xaya na qasa ba tare da haqqinsa
ba, to za a rataya masa shi tun daga qasan-bakwai ranar alqiyama”. Sannan ya ce, “Ya Ubangiji idan
qarya take, to ka makantar da ita, kuma ka sanya qabarinta a cikin gidanta. Sai ta makance, kuma ta
faxa wata rijiyarta a cikin gidanta ta mutu.
Hakanan Abu Mu’awiya Al’aswad a lokacin gwabzawa da Rumawa, wani kafiri daga kafiransu
ya fito. Wanda cutarsa to tsananta ga Musulmi, sai wani daga cikin musulmi ya zo masa (shi Mu’awiya)
sai ya ce “Wannan ya aikata kaza da kaza, ka roqi Allah a kansa». Sai ya xauki mashinsa ya yi addu’a
ya ce, “Kuma ba ka yi jifa ba yayin da ka yi jifa sai dai Allah shi ne ya yi jifa”. Sannan ya ce “Ina
kuke so? Suka ce “Mazakutarsa” Sai suka jefa shi, kuma ba su kuskure gurin da suka faxa ba. Sai ya
kashe maqiyin Allah (S.W.T).
Wasu mutane ba su gushe ba suna cewa, “Mun yi ta yin addu’a amma ba a amsa mana ba. Don
haka mu ba mu ga amfaninta ba». Alhali ba su san cewa su ne ba su cika sharuxxan amsa addu’ar ba.
Kuma su sun vata hanyar addu’ar, da kavar addu’ar zuwa ga Allah Mai Buwaya da xaukaka, saboda
raunin yaqini da raunin imani, baya ga kau da kai ga barin biyayya da afkawa cikin savo.
Ya ku bayin Allah! Ya wajaba musan haqiqanin addu’a da muhimmancinta da girmanta a cikin
wannan addinin kuma cewa, ita alama ce ta kamalar bautar bawa ga Ubangijinsa, kuma mu lazimci
hanya madaidaciyya cikin addu’armu. Mu koyi sonnonin Annabi da ladubban shari’a a cikinta, in
mun yi haka Allah zai sanya mu cikin waxanda ake amsa addu’o’in su ya karvi qasqan da kanmu, da hausaminbar.com
www.hausaminbar.com

Thursday, 3 December 2015

BAYANIN ZAKKA DA YADDA AKEYINTA DA WADANDA SUKA WAJABA SUYITA


BAYANIN ZAKKA DA YADDA AKEYINTA
DA WADANDA SUKA WAJABA SUYITA
Dukkan yabo da godiya da kirari sun tabbata ga Allah, taimakonsa da gafararsa muke nema,
kuma muna neman tsarinsa daga shirrin kawukanmu da munanan ayyukanmu. Wanda Allah ya shiryar babu mai vatar da shi, wanda kuma ya vatar to babu mai shiryar da shi. Kuma ina shaidawa babu abin bauta da gaskiya sai Allah, shi kaxai ne ba shi da abokin tarayya. Kuma ina shaidawa cewa, Annabi Muhammad bawansa ne manzonsa ne. (Ya ku waxanda suka yi imani ku ji tsoron yadda ya cancaci a ji tsoronsa, kada ku mutu face kuna musulmi). (Ya ku mutane ku ji tsoron Ubangijinku wanda ya halicceku daga rai guda xaya, kuma ya ya halicci matarsa daga gare shi, kuma ya yaxa maza da mata daga garesu (su biyu). Ku ji tsoron Allah wanda kuke yiwa junanku magiya da shi, (kuma ku kiyaye) zumunci. Lalle Allah mai kula ne da ku). (Ya ku wanxanda suka yi imani ku ku ji tsoron Allah kuma ku faxi magana ta daidai. Sai Allah ya gyara muku ayyukanku, kuma ya gafarta muku zunubbanku. Wanda ya bi Allah da Manzonsa haqiqa ya rabauta rabauta mai girma). Bayan haka, lalle mafi gaskiyar magana maganar Allah, kuma mafi kyawon shiriya shiriyar Annab Muhammad
صلى الله عليه وسلم) ).
 Kuma mafi shirrin al'amura (a addini) qagaggunsu, kuma duk wani qagaggen abu (addini) bidi'a ce, duk wata bidi'a vata ce, duka wani vata kuma yana wuta. Bayin Allah : waye a cikinmu baya son a qara masa arziqinsa, dukiyarsa ta qaru? Allah ya tsarkake masa ita, ya yi masa albarka a cikinta? To ku taho zuwa ga abin yake sanya haka, wannan abu ba komai ba ne face bayar da zakka. Wannan ibadar ta dukiya da Allah Maxaukakin Sarki ya wajabta
ta akan bayinsa, don haka – Yaku bayin Allah – ku bayar da abin da Allah ya wajabta muku a cikin dukiyoyinku, wadda Allah ya azurta da ita, haqiqa ya fitar da ku daga cikin iyayenku baku da komai, baku san komai ba, ba kwa mallakar amfani ko cutarwa ga kawunanku, sannan ya azurta ku, ya baku abin da baku tava tunanin samunsa ba, don haka ku gode masa, ku bayar da abin da ya wajabta muku, don ku samu kuvuta, kuma dukiyoyinku su tsarkaka. Ku nisanci rowa da son kai da abin da Allah ya wajabta muku, saboda hakan halaka ne, kuma zare albarkar dukiyarku ne. Ku saurara mafi girman abin da Allah ya wajabta muku a cikin dukiyoyinku shi ne bayar da zakka, wadda take rukuni ne na uku a musulunci, kuma abokiyar haxin sallah ce a cikin Alkur’ani. Sannan ta wajaba akan dukkan musulmi baligi xa, mai hankali, wanda ya mallaki abin da ya kai zakka cikakkiyar mallaka.


MANUFOFINTA
• Bayanin wajabcin bayar da zakka, da irin dukiyoyin da ake bada zakka a cikinsu.
• Bayanin ta’asirin zakka a cikin al’umma.
• Tsoratarwa daga hana zakka.
• Bayanin hikomomin wajabta bayar da zakka.
Huduba Ta Farko
ZAKKA DA GUDUMMAWAR DA TAKE
BAYARWA WAJEN TAIMAKON AL’UMMA
Allah Maxaukakin Sarki ya wajabta ta a cikin littafinsa mai girma, inda yake cewa :
[ البقرة : ۱۱۰ ] L r q p o n m l k M
 Ma’ana : «Ku tsayar da sallah ku bayar da zakka ku yi ruku’u da masu ruku’u» (Al- Baqara 43).
Ya sake cewa :
.[ البقرة : ۱۱۰ ] L n m l k M
Ma’ana : “Ku tsaida sallah ku bayar da zakka” (Al-baqra : 110). Haka umarni da bayar da zakka
da yin sallah ya yi ta maimaituwa a cikin Alqur’ani har sama da aya (80).
Hakanan Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم) ya bayyana wa al’ummarsa wajabcinta. An karvo daga Abdullahi
xan Umar – Allah ya yarda da shi – ya ce, Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم) ya ce, “An gina musulunci a bisa
abubuwa biyar, akan a kaxaita Allah, da tsaida sallah, da bayar da zakka, da azumin watan Ramadan,
da hajji” Bukhari da Muslim ne suka rawaito.
Lamarin zakka bai tsaya nan ba, sai da Allah Maxaukakin Sarki ya yi kashedi mai tsanani akan
duk wanda yake hana zakka, Allah ya ce:
Ý ÜÛ Ú Ù Ø × Ö ÕÔ Ó Ò Ñ ÐÏ Î Í Ì Ë Ê É È Ç Æ Å Ä M
.[ ل عمران: ۱۸۰ ] L æ å ä ã â áà ß Þ
Ma’ana : “kada waxanda suke rowa da abin da Allah ya basu na falalarshi su yi zaton haka
alheri ne garesu, a’a hakan sharri ne a garesu, za a naxa musu abin da suka yi rowa da shi ranar
alqiyama. Gadon sammai da qassai duk mallakar Allah ne. kuma Allah masani ne dangane da abin da
kuke aikatawa”. (Al –Imran : 180).
Ya sake cewa a wurin :
.[ التوبة: ۳٤ ] L ^ ] \ [ Z Y X W V U T S R M
Ma’ana : «Waxanda suke taskake zinare da azurfa ba sa ciyar da su saboda Allah, ka yi musu
bushara da azaba mai tsanani. Ranar da xumama musu ita a cikin wutar Jahannama, a naxe goshinsu da gefensu da bayansu da ita, a ce musu wannan shi ne abin da kuka taskake wa kawunanku, ku xanxani abin da kuke taskakewa». (Attauba )
Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم) ya fassara ayar farko da faxinsa : “Duk wanda Allah ya bashi dukiya, amma bai bayar da zakkarta ba, za a mayar masa da wannan dukiya ta zama maciji, wanda baya da gashi a kansa saboda yawan dafinsa, a rataya masa shi, yana cafkar muqamuqinsa, yana cewa : “Ni ne dukiyarka, ni ne abin da ka taskake” Bukhari ne ya rawaito.
Yaku musulmi : Ku sani cewa zakka tana da fa’idoji a addinance da xabi’ance cikin al’umma
masu yawa, ga kaxan daga cikinsu :
1. Bayar da zakka tsaida xaya daga cikin rukunan addinin musulunci ne, wanda a kansu
arziqin bawa yake duniya da lahira.
2. Yin zakka yana kusantar da bawa ga Ubangijinsa, kuma tana qara imani, kamar yadda
sauran ibadu suke kusantar da bawa ga Allah.
3. Abin da yake biyo bayan bayar da zakka na lada mai yawa, Allah yana cewa :
.[ البقرة: ۲۷٦ ] L X W V U T M
“Allah yana shafe albarkar riba, yana renon sadaka” (Albaqra : 276). A wani wurin ya ce,
L μ ´ ³ ² ± ° ¯ ® ¬ « ª ©¨ § ¦ ¥ ¤ £ ¢ ¡ ے ~ } | M
۰[ [الروم: ۳۹
“Duk abin da kuka bayar na haramun don ya qaru a dukiyar mutane, to ba zai qaru a wurin Allah
ba, abin da kuka bayar na sadaka kuna nemar yardar Allah to wannan shi ne mai ninkuwa” (Arrum :
39).
Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم) ya ce, “Wanda ya yi sadaka da kwatankwacin dabino, daga tsakaken abin ya samu – Allah ba ya karva abu sai mai tsarki – to Allah yana karvar wannan sadakar da hannun damansa, ya reneta kamar yadda xayanku yake renon xan goxiyarsa, har ta zama kamar girman dutse”. Bukhari da Muslim ne suka rawaito.
1. Allah yana kankare zunubai da ita, kamar yadda Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم) yake cewa “Sadaka tana kankare zunubai kamar yadda ruwa yake bice wuta”. Anan ana nufin sadakar nafila da ta farilla (zakka).
Daga cikin fa’idojin zakka na gyaran halaye da take kawo wa, akwai :
1. Zakka tana sanya mai yinta ya zama mai karamci da kyauta da rangwame.
2. Zakka ta kan sa mai yin ta, ya zama mai tausayi da jin qai ga ‘yan uwansa miskinai.
Masu jinqai kuwa Allah mai rahama yana jin qansu.
3. Abu ne wanda ake gani bada dukiya da jiki ya kan kawo yalwar qirji, da buxewar
zuciya, da nutsuwa, kuma yana sanya mutum ya zama abin qauna a wurin ‘yan uwansa
musulmai saboda irin amfanin da yake yi wa ‘yan uwansa.
4. Zakka tana tsarkake mai yin ta daga rowa da son kai, kamar yadda Allah ya ce,
.[ التوبة: ۱۰۳ ] L | { z y xw v u t sr q p o n m l k j M
«Ka karvi sadaka daga dukiyoyinsu wadda zaka tsarkake su ka gyara su da ita».
A Bangaren zamantakewa kuwa, Zakka tana bada gudummawa mai yawa daga ciki akwai:
1. A cikinta akwai kawar wa talakawa buqatunsu, waxanda su suka fi yawa a cikin mafi
yawan garuruwa.
2. A cikin zakka akwai qarfafa musulmi, da xaukaka su, don haka ya halatta a bada zakka
don yin jihadi saboda Allah.
3. Zakka tana kawar da gaba da hassada da qyashi da suke cikin zukatan talakawa da
miskinai, saboda idan talakawa na ganin masu hali da dukiya suna walwala a cikin
dukiyarsu, kuma ba sa amfanarsu da ita, da kaxan koda da yawa, to wannan zai iya
jawo gaba da qulli ga mawadata, saboda basu kiyaye haqqinsu ba, ba su biya musu
buqatunsu ba. Amma ida mawadata suka bada wani ‘yanki na dukiyarsu ga talakawa a
farkon shekara, sai waxannan abubuwa su gushe, a samu soyayya da haxuwa da juna.
4. A cikin zakka akwai qaruwar dukiya da yawaita albarkarta, kamar yadda hadisi ya
nuna.
5. A cikin zakka akwai faxaxa dukiya da yaxata, saboda dukiya idan aka sarrafa wani abu
daga cikinta, sai ta qara buxewa, mutane da yawa su amfanu da ita, savanin idan ta
zama tana jujjuyawa tsakanin mawadata kaxai, talakawa ba sa samun komai.
Waxannan fa’idoji gaba xaya suna cikin zakka, kuma suna nuna zakka wani abu ne da yake
lallai a same shi don gyara xaixaikun mutane da al’umma. Tsarki ya tabbata ga Allah Masani Mai hikima.
‘Yan uwa muslmi : ku sani zakka tana wajaba ne a cikin wasu abubuwa kevantattu kamar haka :
1. Kayan da aka tanda don kasuwanci, gidaje ne ko motoci ko dabbobi ko wasu tufafi
da sauran nau’ikan dukiya, abin da za a bayar na wajibi a ciki shi ne za a kasa dukiyar
goma, a xau kashi xaya a kasa shi huxu sai a bada kashi xaya, Mai kayan zai qimanta
shi a farkon kowace shekara ya bada abin da ya cancanta. Amma abin da ya tanada don
buqatarsa, ko don yin haya da shi, daga gidaje ko motoci da sauran abin da aka tanada,
to babu zakka a cikinsa, saboda Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم) yana cewa : “Babu zakka akan musulmi cikin bayinsa da dokinsa (abin hawansa)”. Imam Ahmad ne ya rawaito shi.
2. Abu na biyu da ake fitar wa da zakka shi ne zinare da azurfa ko abin da yake a matsayinsu
wajen zama kuxin abubuwa, idan mutum ya mallaki nisabi, kuma shekara ta zagayo
a kansa bai ragu ba, to wajibi ne ya lissafa abin da yake da shi ya kasa arba’in ya bada
kaso xaya.
3. Abu na uku da ake fitarwa da zakka : kayan gona, duk wanda ya noma abin da ake ci
kuma ana iya ajiye shi, sannan ya kai wisqi sittin, to wajibi ne ya bada zakkarsa anan
take. Waxannan su ne abubuwan da ake fitar wa da zakka, koma bayansu na abin da mutum ya mallaka, na kayan amfanin yau da kullum, kamar motar da yake hawa, ko tufafin da yake sanyawa, da makamantansu to babu zakka a cikinsu. Yaku bayin Allah : Musulmi nagari shi ne wanda yake kallon dukiyar da Allah ya bashi a matsayin amana, da Allah ya bashi, ya kuma dace ya bada haqqinta, ya yi amfani da ita cikin abin da Allah ya yarda da shi. Ba musulmi nagari ba ne wanda yake xaukar dukiyarsa a matsayin wani abu nashi na dole da ya wajaba Allah ya bashi, kuma yake mata kallon dauwama da rashin qarewa, haqiqa
duk wanda ya zama haka to ya yi hasara duniya da lahira. Muna roqon Allah ya kare mu.
Allah ya yi mana albarka cikin abin da muka ji, daga Alqur’ani da Sunnah, ya yi mana gafara,
haqiqa shi mai iko ne akan komai.

Ya ‘yan uwa : Allah Maxaukakin Sarki ya jivinci bayanin waxanda za a bawa zakka a cikin
Alqur’ani mai girma, inda yake cewa :
ے ¡¢ ~ } | { z y x w v u t s r q M
.[ التوبة: ٦۰ ] L ª © ¨ § ¦¥ ¤ £
Ma’ana : «Kaxai sadaka (wato zakka, haqqi ne na) faqirai da miskinai da masu aiki a kanta, da
waxanda ake janyo zukatansu, da bayi, da waxanda ake bi bashi, da kuma saboda Allah da matafiya,
wajibi ne daga wajen Allah, Allah masani ne mai hikima» (Attauba : 60).
www.hausaminbar.com
287
Waxannan sune sinfi takwas da ake bawa zakka : ga bayaninsu xaya
bayan xaya :
1. Faqirai, su ne waxanda ba sa samun abin da zai ishe su, sai xan kaxan wanda bai kai
rabi ba, idan ya zama mutum bai mallaki abin da zai iya ciyar da iyalisa ba na wata shida
to shi faqiri ne, ya halatta a bashi abin da zai ishe shi da iyalansa tsawon shekara.
2. Miskinai : su ne waxanda suke da rabin abin da zai ishe su, ko fiye da rabin, amma ba
su da abin da zai ishe su shekara guda, don haka sai a cika musu na shekara guda.
3. Masu aiki a kan zakkar : su ne waxanda shugaba yake wakilta wa don karvo zakkar daga
mawadata, sannan su raba ta ga waxanda suka cancanta, su kiyayeta, To waxannan ya
halatta a basu zakka gwargwadon aikinsu koda kuwa suna da watada da hali.
4. Waxanda ake son a ja zukatansu zuwa ga musulunci : su ne shugabannin qabilu,
waxanda imaninsu bai yi qarfi ba, ya halatta a basu zakka don qarfafa musu imaninsu,
su zama masu kira zuwa ga addinin Allah. Idan mutum yana da raunin imani kuma
baya cikin shugabannin da ake yi wa biyayya, kawai yana cikin gama – garin mutane,
to shin za a bahi zakka don qarfafa imaninsa, ko kuwa? malamai sun yi savani wajen
ba shi zakka!?.
5. Bayi : wannan ya haxa da sayen bayi da ‘yanta su da kuxin zakka, da fanso ribatattun
musulmi daga wurin kafirai, dak da kuxin zakka.
6. Waxanda ake bi bashi : idan ba su abin da zasu biya bashinsu da shi, to irin waxannan
ya halatta a basu abin da zasu biya bashinsu da shi, bashin mai yawa ne ko kaxan, ko da
kuwa suna da wadatar abin za su ci, misali da za a qaddara cewa ga wani mutum yana
da inda yake samun abincinsa da na iyalansa, amma ana bin shi bashi wanda ba zai iya
biya ba, to za a bashi abin zai biya masa bashinsa daga cikin zakka. Ba ya halatta wanda
yake bin wani bashi ya sauke masa bashin da abin da ya yi niyya na zakka.
7. Wajen xaukaka kalmar Allah : wato jihadi don xaukaka kalmar Allah, za baiwa masu
jihadi abin da zai ishe su daga zakka don fita zuwa jihadi, a sayi kayan jihadi daga
cikin kuxin zakka. Yana cikin Fisabilillahi neman ilimin addini, za a bawa xalibin
da yake neman ilimin addini abin da zai iya neman ilimi da shi, daga littattafai da
makamantansu, sai dai idan yana dukiyar da zai iya samun abin da yake so.
8. Matafiyi : shi ne wanda guzuri ya yanke masa, sai a bashi abin da zai kai shi gida daga
cikin zakka.
Waxannan su ne waxanda Allah ya ambata a cikin littafinsa, ya kuma bawa waxannan wajibi
ne da ya fito daga gare shi a kan ilimi da hikima. Allah Masani ne mai hikima.
Ba ya halatta a sarrafa zakka a cikin waxanda ba waxannan ba, kamar gina masallaci, ko gyara hanya, saboda Allah ya faxi waxanda suka cancanci zakka a keve, keve abu kuwa yana kore shi daga wanda ba shi ba.
Ku ji tsoron Allah – Yaku bayin Allah – ku yi wa kanku hisabi, ku yi adalci, kada ku zaton
zakka tara ce ko hasara ce a kanku, a’a wallahi zakka ganima ce da riba ga wanda ya yi ta, kuma xaya ce daga cikin rukunan musulunci, abokiyar sallah ce a cikin littafin Allah. Aiki da ita aiki ne da rukuni mai girma daga rukunan musulunci, sannan tsarki ce daga savo da zunubi ga wanda ya bayar da ita, tsarkake wa ce garehi da ayyukansa, kuma albarka ce da qaruwa a cikin dukiyarsa.
Allah Maxaukakin Sarki ya ce :
w v u t s r q po n m l k j i h g f e d c M
°¯ ® ¬ « ª ©¨ § ¦ ¥ ¤ £ ¢ ¡ ے ~ } |{ z y x
.[۲٦۸ - البقرة : ۲۷۸ ] L ´ ³ ² ±
Ma’ana : “Yaku waxanda ku ka bada gaskiya ku ciyar daga daxaxan abubuwan da kuka tsururuta da abin da muka fitar muku da cikin qasa, kada ku nufi mummuna ku ciyar daga cikinsa, alhali ku ba za ku karve shi ba idan an baku, sai da rintse idanu, ku sani lallai Allah mawadaci ne abin yabo. (Kusani) Shaixan yana muku alqawarin talauci da rowa (idan kun bayar da abin da kuke da shi) Allah kuwa yana muku alqawarin gafara da falala. Allah mai yalwa ne kuma masani”. (Albaqra : 267 ).