BAYANIN ZAKKA DA YADDA AKEYINTA
DA WADANDA SUKA WAJABA SUYITA
Dukkan yabo da godiya da kirari sun tabbata ga Allah, taimakonsa
da gafararsa muke nema,
kuma muna neman tsarinsa daga shirrin kawukanmu da munanan
ayyukanmu. Wanda Allah ya shiryar babu mai vatar da shi, wanda kuma ya vatar to
babu mai shiryar da shi. Kuma ina shaidawa babu abin bauta da gaskiya sai
Allah, shi kaxai ne ba shi da abokin tarayya. Kuma ina shaidawa cewa, Annabi
Muhammad bawansa ne manzonsa ne. (Ya ku waxanda suka yi imani ku ji tsoron
yadda ya cancaci a ji tsoronsa, kada ku mutu face kuna musulmi). (Ya ku mutane
ku ji tsoron Ubangijinku wanda ya halicceku daga rai guda xaya, kuma ya ya
halicci matarsa daga gare shi, kuma ya yaxa maza da mata daga garesu (su biyu).
Ku ji tsoron Allah wanda kuke yiwa junanku magiya da shi, (kuma ku kiyaye)
zumunci. Lalle Allah mai kula ne da ku). (Ya ku wanxanda suka yi imani ku ku ji
tsoron Allah kuma ku faxi magana ta daidai. Sai Allah ya gyara muku ayyukanku,
kuma ya gafarta muku zunubbanku. Wanda ya bi Allah da Manzonsa haqiqa ya
rabauta rabauta mai girma). Bayan haka, lalle mafi gaskiyar magana maganar
Allah, kuma mafi kyawon shiriya shiriyar Annab Muhammad
صلى الله عليه
وسلم) ).
Kuma mafi shirrin al'amura
(a addini) qagaggunsu, kuma duk wani qagaggen abu (addini) bidi'a ce, duk wata
bidi'a vata ce, duka wani vata kuma yana wuta. Bayin Allah : waye a cikinmu
baya son a qara masa arziqinsa, dukiyarsa ta qaru? Allah ya tsarkake masa ita,
ya yi masa albarka a cikinta? To ku taho zuwa ga abin yake sanya haka, wannan
abu ba komai ba ne face bayar da zakka. Wannan ibadar ta dukiya da Allah
Maxaukakin Sarki ya wajabta
ta akan bayinsa, don haka – Yaku bayin Allah – ku bayar da abin da
Allah ya wajabta muku a cikin dukiyoyinku, wadda Allah ya azurta da ita, haqiqa
ya fitar da ku daga cikin iyayenku baku da komai, baku san komai ba, ba kwa
mallakar amfani ko cutarwa ga kawunanku, sannan ya azurta ku, ya baku abin da
baku tava tunanin samunsa ba, don haka ku gode masa, ku bayar da abin da ya
wajabta muku, don ku samu kuvuta, kuma dukiyoyinku su tsarkaka. Ku nisanci rowa
da son kai da abin da Allah ya wajabta muku, saboda hakan halaka ne, kuma zare
albarkar dukiyarku ne. Ku saurara mafi girman abin da Allah ya wajabta muku a
cikin dukiyoyinku shi ne bayar da zakka, wadda take rukuni ne na uku a
musulunci, kuma abokiyar haxin sallah ce a cikin Alkur’ani. Sannan ta wajaba
akan dukkan musulmi baligi xa, mai hankali, wanda ya mallaki abin da ya kai
zakka cikakkiyar mallaka.
MANUFOFINTA
• Bayanin wajabcin bayar da zakka, da irin dukiyoyin da ake bada
zakka a cikinsu.
• Bayanin ta’asirin zakka a cikin al’umma.
• Tsoratarwa daga hana zakka.
• Bayanin hikomomin wajabta bayar da zakka.
Huduba Ta Farko
ZAKKA DA GUDUMMAWAR DA TAKE
BAYARWA WAJEN TAIMAKON AL’UMMA
Allah Maxaukakin Sarki ya wajabta ta a cikin littafinsa mai girma,
inda yake cewa :
[ البقرة : ۱۱۰ ] L r q p o n m l k M
Ma’ana :
«Ku tsayar da sallah ku bayar da zakka ku yi ruku’u da masu ruku’u» (Al- Baqara
43).
Ya sake cewa :
.[ البقرة : ۱۱۰ ] L
n m l k M
Ma’ana : “Ku tsaida sallah ku bayar da zakka” (Al-baqra : 110).
Haka umarni da bayar da zakka
da yin sallah ya yi ta maimaituwa a cikin Alqur’ani har sama da
aya (80).
Hakanan Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم) ya bayyana wa
al’ummarsa wajabcinta. An karvo daga Abdullahi
xan Umar – Allah ya yarda da shi – ya ce, Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم) ya ce, “An gina musulunci a bisa
abubuwa biyar, akan a kaxaita Allah, da tsaida sallah, da bayar da
zakka, da azumin watan Ramadan,
da hajji” Bukhari da Muslim ne suka rawaito.
Lamarin zakka bai tsaya nan ba, sai da Allah Maxaukakin Sarki ya
yi kashedi mai tsanani akan
duk wanda yake hana zakka, Allah ya ce:
Ý ÜÛ Ú Ù Ø × Ö ÕÔ Ó Ò Ñ ÐÏ Î Í Ì Ë Ê É È Ç Æ Å Ä M
.[ ل عمران:
۱۸۰ ] L æ å ä ã â áà ß Þ
Ma’ana : “kada waxanda suke rowa da abin da Allah ya basu na
falalarshi su yi zaton haka
alheri ne garesu, a’a hakan sharri ne a garesu, za a naxa musu
abin da suka yi rowa da shi ranar
alqiyama. Gadon sammai da qassai duk mallakar Allah ne. kuma Allah
masani ne dangane da abin da
kuke aikatawa”. (Al –Imran : 180).
Ya sake cewa a wurin :
.[ التوبة: ۳٤ ] L ^ ] \ [ Z Y X W V U T S R M
Ma’ana : «Waxanda suke taskake zinare da azurfa ba sa ciyar da su
saboda Allah, ka yi musu
bushara da azaba mai tsanani. Ranar da xumama musu ita a cikin
wutar Jahannama, a naxe goshinsu da gefensu da bayansu da ita, a ce musu wannan
shi ne abin da kuka taskake wa kawunanku, ku xanxani abin da kuke taskakewa».
(Attauba )
Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم) ya fassara ayar
farko da faxinsa : “Duk wanda Allah ya bashi dukiya, amma bai bayar da zakkarta
ba, za a mayar masa da wannan dukiya ta zama maciji, wanda baya da gashi a
kansa saboda yawan dafinsa, a rataya masa shi, yana cafkar muqamuqinsa, yana
cewa : “Ni ne dukiyarka, ni ne abin da ka taskake” Bukhari ne ya rawaito.
Yaku musulmi : Ku sani cewa zakka tana da fa’idoji a addinance da
xabi’ance cikin al’umma
masu yawa, ga kaxan daga cikinsu :
1. Bayar da zakka tsaida xaya daga cikin rukunan addinin musulunci
ne, wanda a kansu
arziqin bawa yake duniya da lahira.
2. Yin zakka yana kusantar da bawa ga Ubangijinsa, kuma tana qara
imani, kamar yadda
sauran ibadu suke kusantar da bawa ga Allah.
3. Abin da yake biyo bayan bayar da zakka na lada mai yawa, Allah
yana cewa :
.[ البقرة: ۲۷٦ ] L X W V U T M
“Allah yana shafe albarkar riba, yana renon sadaka” (Albaqra :
276). A wani wurin ya ce,
L μ ´ ³ ² ± ° ¯ ® ¬ « ª ©¨ § ¦ ¥ ¤ £ ¢ ¡ ے ~ }
| M
۰[ [الروم: ۳۹
“Duk abin da kuka bayar na haramun don ya qaru a dukiyar mutane,
to ba zai qaru a wurin Allah
ba, abin da kuka bayar na sadaka kuna nemar yardar Allah to wannan
shi ne mai ninkuwa” (Arrum :
39).
Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم) ya ce, “Wanda ya yi
sadaka da kwatankwacin dabino, daga tsakaken abin ya samu – Allah ba ya karva
abu sai mai tsarki – to Allah yana karvar wannan sadakar da hannun damansa, ya
reneta kamar yadda xayanku yake renon xan goxiyarsa, har ta zama kamar girman dutse”.
Bukhari da Muslim ne suka rawaito.
1. Allah yana kankare zunubai da ita, kamar yadda Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم) yake cewa “Sadaka tana kankare zunubai kamar yadda ruwa yake
bice wuta”. Anan ana nufin sadakar nafila da ta farilla (zakka).
Daga cikin fa’idojin zakka na gyaran halaye da take kawo wa, akwai
:
1. Zakka tana sanya mai yinta ya zama mai karamci da kyauta da
rangwame.
2. Zakka ta kan sa mai yin ta, ya zama mai tausayi da jin qai ga
‘yan uwansa miskinai.
Masu jinqai kuwa Allah mai rahama yana jin qansu.
3. Abu ne wanda ake gani bada dukiya da jiki ya kan kawo yalwar
qirji, da buxewar
zuciya, da nutsuwa, kuma yana sanya mutum ya zama abin qauna a
wurin ‘yan uwansa
musulmai saboda irin amfanin da yake yi wa ‘yan uwansa.
4. Zakka tana tsarkake mai yin ta daga rowa da son kai, kamar
yadda Allah ya ce,
.[ التوبة: ۱۰۳ ] L | { z y xw v u t sr q p o n m l k j M
«Ka karvi sadaka daga dukiyoyinsu wadda zaka tsarkake su ka gyara
su da ita».
A Bangaren zamantakewa kuwa, Zakka tana bada gudummawa mai yawa daga
ciki akwai:
1. A cikinta akwai kawar wa talakawa buqatunsu, waxanda su suka fi
yawa a cikin mafi
yawan garuruwa.
2. A cikin zakka akwai qarfafa musulmi, da xaukaka su, don haka ya
halatta a bada zakka
don yin jihadi saboda Allah.
3. Zakka tana kawar da gaba da hassada da qyashi da suke cikin
zukatan talakawa da
miskinai, saboda idan talakawa na ganin masu hali da dukiya suna
walwala a cikin
dukiyarsu, kuma ba sa amfanarsu da ita, da kaxan koda da yawa, to
wannan zai iya
jawo gaba da qulli ga mawadata, saboda basu kiyaye haqqinsu ba, ba
su biya musu
buqatunsu ba. Amma ida mawadata suka bada wani ‘yanki na dukiyarsu
ga talakawa a
farkon shekara, sai waxannan abubuwa su gushe, a samu soyayya da
haxuwa da juna.
4. A cikin zakka akwai qaruwar dukiya da yawaita albarkarta, kamar
yadda hadisi ya
nuna.
5. A cikin zakka akwai faxaxa dukiya da yaxata, saboda dukiya idan
aka sarrafa wani abu
daga cikinta, sai ta qara buxewa, mutane da yawa su amfanu da ita,
savanin idan ta
zama tana jujjuyawa tsakanin mawadata kaxai, talakawa ba sa samun
komai.
Waxannan fa’idoji gaba xaya suna cikin zakka, kuma suna nuna zakka
wani abu ne da yake
lallai a same shi don gyara xaixaikun mutane da al’umma. Tsarki ya
tabbata ga Allah Masani Mai hikima.
‘Yan uwa muslmi : ku sani zakka tana wajaba ne a cikin wasu
abubuwa kevantattu kamar haka :
1. Kayan da aka tanda don kasuwanci, gidaje ne ko motoci ko
dabbobi ko wasu tufafi
da sauran nau’ikan dukiya, abin da za a bayar na wajibi a ciki shi
ne za a kasa dukiyar
goma, a xau kashi xaya a kasa shi huxu sai a bada kashi xaya, Mai
kayan zai qimanta
shi a farkon kowace shekara ya bada abin da ya cancanta. Amma abin
da ya tanada don
buqatarsa, ko don yin haya da shi, daga gidaje ko motoci da sauran
abin da aka tanada,
to babu zakka a cikinsa, saboda Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم) yana cewa : “Babu zakka akan musulmi cikin bayinsa da dokinsa
(abin hawansa)”. Imam Ahmad ne ya rawaito shi.
2. Abu na biyu da ake fitar wa da zakka shi ne zinare da azurfa ko
abin da yake a matsayinsu
wajen zama kuxin abubuwa, idan mutum ya mallaki nisabi, kuma
shekara ta zagayo
a kansa bai ragu ba, to wajibi ne ya lissafa abin da yake da shi
ya kasa arba’in ya bada
kaso xaya.
3. Abu na uku da ake fitarwa da zakka : kayan gona, duk wanda ya
noma abin da ake ci
kuma ana iya ajiye shi, sannan ya kai wisqi sittin, to wajibi ne
ya bada zakkarsa anan
take. Waxannan su ne abubuwan da ake fitar wa da zakka, koma
bayansu na abin da mutum ya mallaka, na kayan amfanin yau da kullum, kamar
motar da yake hawa, ko tufafin da yake sanyawa, da makamantansu to babu zakka a
cikinsu. Yaku bayin Allah : Musulmi nagari shi ne wanda yake kallon dukiyar da
Allah ya bashi a matsayin amana, da Allah ya bashi, ya kuma dace ya bada
haqqinta, ya yi amfani da ita cikin abin da Allah ya yarda da shi. Ba musulmi
nagari ba ne wanda yake xaukar dukiyarsa a matsayin wani abu nashi na dole da
ya wajaba Allah ya bashi, kuma yake mata kallon dauwama da rashin qarewa,
haqiqa
duk wanda ya zama haka to ya yi hasara duniya da lahira. Muna
roqon Allah ya kare mu.
Allah ya yi mana albarka cikin abin da muka ji, daga Alqur’ani da
Sunnah, ya yi mana gafara,
haqiqa shi mai iko ne akan komai.
Ya ‘yan uwa : Allah Maxaukakin Sarki ya jivinci bayanin waxanda za
a bawa zakka a cikin
Alqur’ani mai girma, inda yake cewa :
ے
¡¢ ~ } | { z y x w v u t s r q M
.[ التوبة: ٦۰ ] L ª © ¨ § ¦¥ ¤ £
Ma’ana : «Kaxai sadaka (wato zakka, haqqi ne na) faqirai da
miskinai da masu aiki a kanta, da
waxanda ake janyo zukatansu, da bayi, da waxanda ake bi bashi, da
kuma saboda Allah da matafiya,
wajibi ne daga wajen Allah, Allah masani ne mai hikima» (Attauba :
60).
www.hausaminbar.com
287
Waxannan sune sinfi takwas da ake bawa zakka : ga bayaninsu xaya
bayan xaya :
1. Faqirai, su ne waxanda ba sa samun abin da zai ishe su, sai xan
kaxan wanda bai kai
rabi ba, idan ya zama mutum bai mallaki abin da zai iya ciyar da
iyalisa ba na wata shida
to shi faqiri ne, ya halatta a bashi abin da zai ishe shi da
iyalansa tsawon shekara.
2. Miskinai : su ne waxanda suke da rabin abin da zai ishe su, ko
fiye da rabin, amma ba
su da abin da zai ishe su shekara guda, don haka sai a cika musu
na shekara guda.
3. Masu aiki a kan zakkar : su ne waxanda shugaba yake wakilta wa
don karvo zakkar daga
mawadata, sannan su raba ta ga waxanda suka cancanta, su kiyayeta,
To waxannan ya
halatta a basu zakka gwargwadon aikinsu koda kuwa suna da watada
da hali.
4. Waxanda ake son a ja zukatansu zuwa ga musulunci : su ne
shugabannin qabilu,
waxanda imaninsu bai yi qarfi ba, ya halatta a basu zakka don
qarfafa musu imaninsu,
su zama masu kira zuwa ga addinin Allah. Idan mutum yana da raunin
imani kuma
baya cikin shugabannin da ake yi wa biyayya, kawai yana cikin gama
– garin mutane,
to shin za a bahi zakka don qarfafa imaninsa, ko kuwa? malamai sun
yi savani wajen
ba shi zakka!?.
5. Bayi : wannan ya haxa da sayen bayi da ‘yanta su da kuxin
zakka, da fanso ribatattun
musulmi daga wurin kafirai, dak da kuxin zakka.
6. Waxanda ake bi bashi : idan ba su abin da zasu biya bashinsu da
shi, to irin waxannan
ya halatta a basu abin da zasu biya bashinsu da shi, bashin mai
yawa ne ko kaxan, ko da
kuwa suna da wadatar abin za su ci, misali da za a qaddara cewa ga
wani mutum yana
da inda yake samun abincinsa da na iyalansa, amma ana bin shi
bashi wanda ba zai iya
biya ba, to za a bashi abin zai biya masa bashinsa daga cikin
zakka. Ba ya halatta wanda
yake bin wani bashi ya sauke masa bashin da abin da ya yi niyya na
zakka.
7. Wajen xaukaka kalmar Allah : wato jihadi don xaukaka kalmar
Allah, za baiwa masu
jihadi abin da zai ishe su daga zakka don fita zuwa jihadi, a sayi
kayan jihadi daga
cikin kuxin zakka. Yana cikin Fisabilillahi neman ilimin addini,
za a bawa xalibin
da yake neman ilimin addini abin da zai iya neman ilimi da shi,
daga littattafai da
makamantansu, sai dai idan yana dukiyar da zai iya samun abin da
yake so.
8. Matafiyi : shi ne wanda guzuri ya yanke masa, sai a bashi abin
da zai kai shi gida daga
cikin zakka.
Waxannan su ne waxanda Allah ya ambata a cikin littafinsa, ya kuma
bawa waxannan wajibi
ne da ya fito daga gare shi a kan ilimi da hikima. Allah Masani ne
mai hikima.
Ba ya halatta a sarrafa zakka a cikin waxanda ba waxannan ba,
kamar gina masallaci, ko gyara hanya, saboda Allah ya faxi waxanda suka
cancanci zakka a keve, keve abu kuwa yana kore shi daga wanda ba shi ba.
Ku ji tsoron Allah – Yaku bayin Allah – ku yi wa kanku hisabi, ku
yi adalci, kada ku zaton
zakka tara ce ko hasara ce a kanku, a’a wallahi zakka ganima ce da
riba ga wanda ya yi ta, kuma xaya ce daga cikin rukunan musulunci, abokiyar
sallah ce a cikin littafin Allah. Aiki da ita aiki ne da rukuni mai girma daga
rukunan musulunci, sannan tsarki ce daga savo da zunubi ga wanda ya bayar da
ita, tsarkake wa ce garehi da ayyukansa, kuma albarka ce da qaruwa a cikin
dukiyarsa.
Allah Maxaukakin Sarki ya ce :
w
v u t s r q po n m l k j i h g f e d c M
°¯
® ¬ « ª ©¨ § ¦ ¥ ¤ £ ¢ ¡ ے ~ } |{ z y x
.[۲٦۸ - البقرة : ۲۷۸ ] L ´
³ ² ±
Ma’ana : “Yaku waxanda ku ka bada gaskiya ku ciyar daga daxaxan
abubuwan da kuka tsururuta da abin da muka fitar muku da cikin qasa, kada ku
nufi mummuna ku ciyar daga cikinsa, alhali ku ba za ku karve shi ba idan an
baku, sai da rintse idanu, ku sani lallai Allah mawadaci ne abin yabo. (Kusani)
Shaixan yana muku alqawarin talauci da rowa (idan kun bayar da abin da kuke da
shi) Allah kuwa yana muku alqawarin gafara da falala. Allah mai yalwa ne kuma
masani”. (Albaqra : 267 ).
No comments:
Post a Comment